A yayinwannan zama na tsawon watanni biyu ‘yan majalisar dokokin kasar ta Nijer zasu tantauna akan wasu mahimman batutuwan da gwamnatin ISUHU MAHAMADU ta gabatar musamman tsarin kasafin kudaden shekarar 2016 da aka kyasta cewa ya haura bilion 1785 na sefa.
ALHAJI YAHUZA SADISU shine ministan sadarwar jamhuriyar Nijer yace.
‘yan adawa wadanda tuni suka fara sukar wannan tsarin kasafi sun bayyana zaman majalisar a matsayin wata damar da zasu yi anfani da ita domin gurfanar da hukumomin jamhuriyar ta 7 kamar yadda dan majalisar dokoki Tijani Abdulkadri na jam’iyyar MNSD ya ce.
Jam’iyar PNDS TARAYYA mai mulkita bakin dan majalisa ASUMANA MALAN ISA ta watsar da wannan zargin.
A yayin bukin bude wannan taro kakakin majalisar dokokin AMADU SALIHU ya bukaci daukacin mahalartan da su yi tsayuwar minti daya domin tunawa da alhazan Nijer da suka rasu a turereniyer MINA da kuma mutane 15 din da wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka kashe a wani kauyen karkarar diffa ran sallar layya da dadare.
Ga rahoton Souly Mummuni Barma.