Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIGER REPUBLIC: Gwamnatin Nijar Ta Sallami Wasu Ministocinta


Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

A wata alama kamar ta baraka gwamnatin Nijar ta kori ministocinta na wasu jam'iyyun kawance.

Sakataren gwamnatin jamhuriyar Nijar Gandu Zakara ya sanarda sauke wasu ministoci daga mukamansu.

Sanarwar tace an rusa ma'aikatar fasalin kasa saboda an sallami shugaban jam'iyyar IDR Ahmadu Bubakar Sesay daga aiki. Sanarwar ta kara da cewa Gambo Habu ya maye gurbin ministan raya al'adu Usman Abdu na jam'iyyar IDR.

A ra'ayin 'yan adawa lamarin wata alama ce ta baraka tsakanin jam'iyyun dake mulkin kasar.

Alhaji Dudu Rahaman sarkin yakin jam'iyyun adawa na ARDR yace mutanen shugaba Muhamadou Issoufou ba mutane ba ne da za'a zauna dasu na tsawon lokaci. Yace su sun zauna dasu shekara uku sun kuma sani. Fitowar Bukar Sesay daga cikin gwamnatin bai basu mamaki ba. Ibrahim Yakuba ma da ya yi masu kokari sun koreshi. Yace dama can sun san akwai rigima ta rarrabuwar kawuna a tafiyar tasu.

Rahman yace ba'a kare fita daga gwamnatin ba. Nan da lokacin zabe sai kowa ya fice an bar 'yan jam'iyyar gwamnati.

Amma Alhaji Asmana Muhammad na jam'iyyar PNDS tarayya mai mulki yace dama ce shugaban kasa ya baiwa Ahmadu Bukar Sesay saboda ya mayar da hankali kan shirin zaben 2016. Yace zargin rabuwar kawuna zance ne kawai na 'yan adawa.

Asmana yace duk wanda ya san shugaban kasa ya san mutum ne mai son a zauna lafiya. Babu yadda za'a yi ya bata yin tafiya tare ko ya ci amanar wanda suke tafiya tare. Yace Sesay yana da tashi jam'iyyar. Babu yadda zai barta domin ya cigaba da rike mukamin minista. Bazu Muhammad ya bar mukaminsa na minista saboda ya yi shirin zabe. Sabo da haka abun da ya faru ba sabon abu ba ne.

To saidai an ce an dade ana ta yada batun rashin jituwa tsakanin minista Ahmadu Bubakar Sesay da Firayim Ministan kasar. Wasu sun ce rikicin ya kawo zaman tankiya yayin wani taron majalisar ministoci har sai da shugaban kasa ya shiga tsaninsu. Bugu da kari aniyar Ahmadu Bukar Sesay na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2016 mai zuwa ta haddasa rashin jituwa tsakaninsa da shugaban kasar na yanzu.

Ga rahoton Sule Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

XS
SM
MD
LG