Wasu takardun sirri, da su ka fada hannun gidan talbijin din Al Jazeera sun tona cewa a yayin tattaunawar shekarar dubu biyu da takwas da ta shekarar dubu biyu da tara mashawartan Falasdinawa sun yi wani tayi a boye na yin gagarumin sassaucin da ya kunshi barwa Israila kusan illahirin gabashin birnin Kudus da suka mamaye.
Takardun bayanan sirrin na wata tattaunawar da aka yi a cikin watan yunin shekarar dubu biyu da takwas tsakanin jami’an Falasdinawa da na Amurka da kuma na Israila sun nuna cewa babban mashawarcin Falasdinawa Ahmed Qurei ya bada shawara a lokacin cewa ban da unguwa daya kawai, Israila ta ci gaba da rike illahirin manyan unguwannin da ta riga ta gine a gabashin birnin Qudus,wanda ta kama a yakin shekarar 1967.
Talbijin din Al Jazeera mai cibiya a kasar Qatar ya ce cikin wasu ‘yan kwanakin da ke tafe zai wallafa sauran takardun da za su yi karin haske akan karin sassaucin da mashawartan Falasdinawan su ka yi game da batutuwa masu sosa zuciya irin su maganar komawar Falasdinawa ‘yan gudun hijira da kuma shawarar da aka bayar cewa a sanya muhimman wuraren ibadar birnin Qudus a karkashin kulawar wasu kasashen duniya.
A cewar takardun sirrin, shugabannin Israila wadanda gwamnatin Amurka ke goyawa baya, sun ki yarda da tayin, da su ka ce bai gamshe su ba.
A wata bayyanar da yayi jiya lahadi ta talbijin din Al-Jazeera, babban