Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kudurin dokar da ya bada damar daukar matakan da Shugaban ya bayyana a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya ranar 29 ga watan Maris, akan matakan da gwamnatinsa ke dauka don yaki da yaduwar cutar coronavirus, da ta zama annoba a duniya baki daya.
Ministan Ma'aikatar Shari’a a Najeriya, kuma babban lauyan gwamnatin kasar, Abubakar Malami, ya ce duba da bayanan da masana ke yi akan muhimmancin takaita cudanya tsakanin al’umma a matsayin hanya mafi sauki mafi gaggawa kuma ta dakile yaduwar cutar coronavirus, hana zirga-zirga mataki ne da ya dace saboda yana da nasaba da annoba.
Malami ya kuma ce dokar da Shugaba Buhari ya sanya wa hannu doka ce wadda ta samo asali daga kundin tsarin mulkin Najeriya, da kuma dokokin kasa-da-kasa da Najeriya ta sanya wa hannu.
Ko da yake wasu masana harkokin shari'a sun yi korafin cewa dokoki basu ba Shugaban kasa ikon daukar matakan da zasu takura wa al'ummar kasa ba ta hanyar takaita musu harkokin yau da kullum, Ministan ya ce tabbas idan babu wani kwakkwaran dalili doka bata ba Shugaban kasa damar daukar wannan matakin ba amma kuma kamar yadda kowanne dan kasa ke da hakkin kai-da-komo, haka kuma kowanne dan kasa ke da hakkin gwamnati ta kare shi daga kamuwa da duk wata annoba, a karkashin dokokin Najeriya da na kasa-da-kasa.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Umar Faruk Musa.
Facebook Forum