A Najeriya, jihar Legas cutar coronavirus ta fara bulla daga bisani kuma ta bayyana a wasu jihohi na yammaci, kudanci, gabashi da kuma arewacin kasar.
Jihar Bauchi ce jihar da cutar ta fara bulla a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya dake da jihohi guda 6.
Jim kadan bayan bullar cutar coronavirus a jihar Bauchi, dukkan gwamnatocin jihohin yankin suka tashi tsaye don aiwatar da matakan dakile yaduwar cutar ta hanyar kafa kwamitocin wayar da kan al’umma da hanyoyin da jama'a zasu bi don kauce wa kamuwa da cutar, da rufe makarantu, da iyakokin jihohin da kuma kasuwanni amma banda wuraren da ake saida kayayyakin bukatun yau da kullum.
Dr. Aliyu Muhammad Maigoro, kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, ya ce ya kamata al’umma su guji shiga cunkoso, kuma su yawaita wanke hannu da tsaftace muhalli.
A jihar Gombe, babban mai ba gwamnan jihar shawara, Alhaji Sama'ila Uba Misilli, ya shaida wa Muryar Amurka cewa gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya ya fitar da kudi sama da naira miliyan dari biyar a matsayin tallafin aikin dakile yaduwar cutar a jihar.
A jihohin Adamawa da Taraba dake makwabtaka da kasar Kamaru, sun dauki matakan rufe kan iyakokinsu a yayin da jihar Adamawa ta sayo wasu na’urori da zasu taimaka wajen ajiye jini kafin a kai wurin gwaji. Jihar Taraba ita kuma ta karfafa toshe duk wata kafa tsakaninta da jihar Benue, kasancewar akwai rahoton bullar cutar a jihar.
Haka kuma a jihar Yobe an dauki matakan tunkarar cutar. Kwamishinan yada labaran jihar Abdullahi Bego, ya ce gwamnatin jihar ta rufe iyakokinta.
A jihar Borno an dauki matakin yaki da cutar coronavirus kamar a sauran jihohin shiyyar arewa maso gabas, musamman a sansanonin 'yan gudun hijira sama da 20 dake dauke da mutane kusan sama da miliyan daya. Wani mazaunin garin Maiduguri ya ce an kai musu na’urorin gwaje-gwaje, sannan ana wayar musu da kai akan muhimmancin wanke hannu da tsafta.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Abdulwahab Muhammed.
Facebook Forum