A daidai lokacin da dokar hana zirga-zirga da tara jama'a a jihar Kaduna ke neman cika mako guda, rundunar 'yan-sandan jihar ta sanar da cafke mutum 165 bisa zargin karya dokar.
Mai magana da yawun rundunar 'yan-sandan ta Kaduna ASP Mohammed Jalige, wanda ya bayyana hakan, ya ce rundunar ta kama motoci da babura sama da 200.
Ya ce “an cafke mutum 165 da suka karya dokar zama a gida, kuma an kwace motoci da keke na pep a kalla 200.”
Ya kuma ce za a kama duk wanda ya kara karya dokar.
Tuni dai aka gurfanar da wasu daga cikin wadanda aka kama gaban kotu a jiya Litinin inji Lauyan gwamnati Dari Bayero.
Barr. Abdulbasid Suleman ne lauyan wadanda gwamnatin Kaduna ke zargi da karya dokar ta hana fita, kuma ya ce ya kamata a bayar da belinsu.
Dokar hana zirga-zirga da tara jama'a a jihar Kaduna dai ta sa wasu sun fara kokawa, in da suke cewa basu da abincin da zasu ci idan basu fita nema ba.
Ya zuwa yanzu dai jihohin arewa da dama sun bi sahun Kaduna wajen hana shiga da fita sai bisa kwakkwaran dalili.
Facebook Forum