A Najeriya, kungiyoyin fararen hula na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da matakan da hukumomi ke dauka na hana zirga-zirga domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.
A baya-bayan nan dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umurnin hana fita a Abuja, Legas da kuma Ogun.
Auwal Musa Rafsanjani, babban jami'i ne a kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, kuma ya yi mana tsokaci kan wannan mataki da hukumomin na Najeriya ke daukawa.
Ya ce “Idan aka rufe mutane ba tare da an tanadar musu da abinci ba, yunwa za ta yi musu illa.”
A cewarsa, “idan ka duba wurare kamar Kano da Legas da kuma Ibadan, cikin gida daya zaka samu mutum 30.”
“Yadda ake cewa kar a yi cudanya da mutane, zama wuri daya da mutane da dama zai yi musu illa da kara janyo wasu cututtuka.”
A cewar Rafsanjani, “hada-hadar kawo abinci tsakanin jihohi na da muhimmanci kuma abin da ya kamata a yi shi ne a tabbatar cewa an samu kayan gwaji ta yadda za a iya duba duk wanda zai shiga kowace jiha domin kai kayayyakin abinci.”
Ya zuwa yanzu an kafa dokar takaita zirga-zirga a birane da kuma jihohi da dama a Najeriyar.
A cewar hukumar dakile cututtuka ta NCDC, mutum 131 ne aka tabbatar cewa suna dauke da cutar a kasar, yayin da cutar ta yi sanadin mutuwar mutum 2.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum