Hukumar tsaron cikin gida ta Amurka ta bayyana rahotonta na karshen shekara ta 2015,wanda ya nuna kokarin hukumar shige da fice wacce take lura da shirin korar bakin hauren bisa la'akari da irin laifuffuka, ko barazana ga zaman lafiya, tsaron kan iyaka, da kuma tsaron kasa.
Hukumar tace, kasa-kasan adadin wadanda take tusa keyarsun, ya ta'aallaka ne kan ragi na kashi 30 cikin dari na kame da hukumar shige da fice take yi daga kan iyakoki, wadda tace ya nuna wadanda suke neman tsallakowa cikin kasar ba bisa ka'ida ba, ya ragu.
A fadin kasa baki daya, wanda ya hada da kame daga kan iyakoki da kuma a nan cikin gida, Amurka ta kori bakin haure dubu dari hudu da sittin da biyu, kasa da mutum dubu 115 idan aka kwatanta da bara.