Jirgin da ya sauka a Koriya ta Kudu a safiyar yau jumma'a, ya samu rakiyar kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma hukumar kare fursunonin yaki POW/MIA.
Dawo da su din da akayi ya soma tabbatar da yarjejeniyar da aka cimma a watan da ya gabata, tsakanin shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da suka yi zaman tattaunawa mai dimbin tarihi a kasar Singapore. Trump yayi amfani da shafin sa na Twitter inda ya yi wa Kim godiya bayan da gawarwakin suka sauka a Koriya ta kudu.
Kimanin sojojin Amurka 7,700 ne suka bace a yakin Koriya kuma ana kyautata zaton mafi yawancin gawarwakin har yazu suna Koriya ta Arewa.
Facebook Forum