Tattalin arzikin Amurka ya yi saurin cigaban da ba a ga irinsa ba tun shekaru hudu da su ka gabata, a cikin watannin Afirilu da Mayu da kuma Yuni na bana.
Rahoton Ma'aikatar Cinakayya na jiya Jumma'a ya ce tattalin arzikin Amurka, wanda shi ne ya fi girma da kuma karfi a duk duniya, ya karu da kashi 4.1% a ma'aunin shekara-shekara a zango na biyu na kwata.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce rage harajin da ya yi da kuma manufofinsa na cinakayya, su ne su ka haifar da wannan cigaban da tattalin arzikin Amurka ya samu.
Facebook Forum