Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa tare da Zaizayar Kasa Ya Hallaka Mutane Fiye da 254 a Colombia


Yadda sojojin Colombia suka dinga ceto wadanda ambaliyar ruwa ta shafa
Yadda sojojin Colombia suka dinga ceto wadanda ambaliyar ruwa ta shafa

A jiya Lahadi, iyalai da masu ceto sun wuni suna neman mutanen da ambaliya da zaizayar kasa ta abka da su a kudancin Colombia inda mutane akalla mutane 254 suka hallaka, ciki har da kanana yara, wasu da dama kuma suka jikata

Shugaban kasar Colombia, Juan Manuel Santos da ya sake zuwa garin na Mocoa jiya Lahadi don ganin yanda ake gudanar ayyukan ceton, ya dora a shafinsa na Twitter cewar alkalumman farko nada damuwa.


Sai dai yace canjin yanayi shine ya yi sanadiyar wannan bala’i inda garin Mocoa ya samu kashi daya cikin uku na ruwan sama da ya saba samu a cikin dare daya.


Shugaba Santos ya mika godiyarsa ga China da bankin raya cikin gida na Amurka da suka taimaka da dala miliyon daya da dala dubu dari biyu don samar da kayan agaji. Haka zalika, Jamus da Belgium kuma sun bada nasu taimako.

Koguna da dama dake kusa da garin Mocoa ne suka batse a jiya da safiyar Asabar, wanda ya yi sanadiyar kwarar ruwa, tabo da kuma tarkace zuwa cikin garin inda suka lalata hanyoyi suka kuma shiga gidaje a lokacin da mutane suka yi bacci

Ma’aikatar sa kai da masu kashe gobara sun tsamo gawarwaki 83 a cikin kwata a garin Villagarzon kuma suka ce har iyau akwai wasu Karin gawarwaki a cikin tarkace.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG