Yayinda yake magana da babban sakataren kungiyar ta OIC Mr. Iyad Ameen Madami Shugaba Buhari ya gargadi kungiyar ta aika da wata tawagar bincike zuwa jihohin Borno, Yobe da Adamawa ta ga irin barnar da kungiyar 'yan ta'adan ta yi.
Shugaba Buhari ya fadawa Mr. Madani cewa tawagar zata taimakawa OIC yanke shawara akan irin taimakon da zata iya ba Najeriya domin farfadowa da sake tsugunar da al'ummomin yankin da suka rasa muhallansu.
Shugaba Buhari ya kara kalubalantar kungiyar ta OIC da ta gaggauta bada taimakonta akan kawo zaman lafiya da tabbatar da doka da oda a kasar Libya wadda yace ta zama kasar da yanzu take da 'yan ta'ada dake haddasa miyagun ayyuka a kasashen yammacin da tsakiyar Afirka tun lokacin da gwamnatin Ghaddafi ta ruguje. Kasar Libya ta zama wata cibiyar harfar da 'yan ta'ada
Shugaba Buhari ya yadda da Mr. Madani cewa 'yan ta'ada dake aikata ta'adanci da sunan addini sun makawa addinin Musulunci wani mugun suna.
Shugaba Buhari yace ta hanyar ilimantar da mutane ne kawai da ingantaccen ilimin addinin Islama zai dakile yaduwar 'yan ta'ada da ta'adanci da sunan Islama. Ingantaccen ilimi ne zai hanasu samun mutane suna shiga kungiyoyinsu.
Saboda haka ya gargadi kungiyar OIC ta taimaki gwamnatin tarayyar Najeriya kawowa kasarsa ilimin gaskiya da wayar da kawunan 'yan Najeriya da gaskiya.