Kwamitin dai ya kunshi ‘yan Majalisar Tarayya da Gwamnoni da Yan Kasuwa da kuma wasu kwararru wajen sake tsugunnar da jama’a. da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin shugaba Buhari yace lalle ayyukan kwamitin zasu tafi ne karkashin jagorancin amintattun mutanen da suka san ya kamata, kuma wayanda an tabbatar zasu yiwa al’umma aiki ba tare da yaudara ko cuta ba karkashin Janal T.Y. Danjuma, kuma aikin zai kasance na shekaru Uku ne kawai.
Shugaba Buhari yace kwamitin zai sami kudin gudanar da ayyukansa na shiga daga gwamnatin Tarayyar Najeriya da jihohi da kananan Hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kungiyoyi na kasashen ketare masu tallafawa inganta rayuwar jama’a.
Kasancewar shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya, kuma mai wakiltar jihar Borno a Majalisa, Sanata Ali Ndume, na daya daga cikin membobin kwamitin, wakilin Muryar Amurka Umar Faruk, ya tuntubeshi kan yadda suke fatan aikin kwamitin zai kasance. Wanda kuma yace zasuyi iyaka kokarinsu don ganin sun taimaka don sun san halin da jama’a ke ciki. Ya kuma ce zasu fara ne da maganar abin da mutane zasu ci a cikinsu kafin aje ga gyaran muhalli.
Shugaban kwamitin Janal T.Y. Danjuma, ya tabbatarwa da shugaba Buhari cewa zasu yi aikinsu bisa ga rikon amana, da tabbatar da cewa sunyi abin da ke dai dai domin fitar da al’ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya daga halin kunci da wahala da suka sami kansu ciki tun lokacin da aka fara yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram.
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.