A cewar Garba Datti Muhammad mutane basu fahimci kudurin ba domin ba wai yana nufin rage ikon shugaban kasa ko gwamnan ba ne.
Kudurin da ya gabatar ya ta'allaka ne akan dokar da ta bada hanyoyin da za'a cire alkalan kotuna. Dokar ta nuna shugaban kasa da 'yan majalisa ko kuma gwamna da tashi 'yan majalisar ne zasu iya cire alkali idan aka samu kuri'u biyu bisa ukku.
Yace hukumar dake hukumta alkalai ko NJC ba'a bata wani matsayi ba akan cire alkalai. Irin wannan ya sa gwamnatin Kwara ta tsige babbar alkaliyar jihar saboda rashin jituwa da suka samu. Gwamna da 'yan majalisa sun cireta saboda sun ce tsarin mulki ya basu damar yin hakan.
Daga baya dai kotun koli tace abun da suka yi ba daidai ba ne saboda haka aka soke korar da aka yi mata. Kotun kolin tace akwai dan kuskure da aka samu a tsarin mulkin Najeriya saboda NJC ce ke kula da alkalai, take horonsu kuma ace bata da na cewa a cirewarsu. Kotun tace hakan ba daidai ba ne.
Hukumcin kotun koli ya zama doka amma kuma kotun bata da hurumin yin doka. Dalili ke nan Datti Muhammad ya ga ya dace ya kawo kudurin da zai maida shari'ar da kotun koli ta yanke ta zama dokar kasa da za'a dinga aiki da ita.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.