A cewar shugaban kwamitin Garba Datti Mohammad, kwamitin zai binciki ko hukumar DSS tana da hurumin da zata aikata hakan. Kwamitin yayi shiri gayyatar tun daga ministan Shari’a zuwa daraktan hukumar DSS da kuma Alkalan da aka kama, sai kuma wasu hukumomi da kungiyoyi.
Wannan mataki da Majalisar ta dauka yasa wasu ‘yan kungiyar lauyoyi ta kasa nuna goyon bayansu akan aikin da kwamitin zai yi. Barista Ralph Agama, lauya mai zaman kansa a Abuja, yace duk matakin da hukumar tsaro ta dauka akan Alkalan ba dai dai bane, hukumar dake kula da ayyukan Alkalan kotuna itace kadai ke da hurumin daukar mataki na horo ko akasin haka akan Alkalai a Najeriya.
A wani zama da Majalisar Wakilai tayi ne dan Majalisa Kingsley Chinda, ya koka akan farmakin da hukumar tsaro ta farin kaya ta kaiwa manyan Alkalai cikin dare, abin da yasa aka kafa wannan kwamiti kenan kuma aka bashi wa’adin makonni Shida da yayi bincike akan al’amarin.
Saurari rahotan Medina Dauda daga Abuja.