Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham yace ‘yan zagon-kasa su na kokarin fakewa da kiraye-kirayen zahiri na sauyi, yana mai cewa babu ta yadda za a iya kawo sauyin ta hanyar yin barna.
Shugaba Assad ya fada cikin wani jawabi ta telebijin ga kasar yau litinin cewa Sham ba zata samu ci gaba ba sai da kwanciyar hankali. Wannan shi ne karo na uku da shugaban yake gabatar da muhimmin jawabi tun lokacin da aka fara gudanar da tunzurin nuna kin jinin gwamnati a tsakiyar watan Maris.
Shugaba Assad yace zai kafa kwamitin da zai nazarci gyare-gyare ga tsarin mulkin Sham, ya kuma yi gargadin cewa abu mafi hatsari da kasar ta ke fuskanta shi ne nakkasa ko kuma lalacewar tattalin arzikinta.
Kafin wannan jawabi nasa, sakataren harkokin wajen Britaniya, William Hague, yayi kira ga shugaban da ya gabatar da sauye-sauye ko kuma ya sauka. Hague yace yana fata kasar Turkiyya zata matsa lamba kan makwabciyarta Sham ta kuma fadawa shugaba Assad cewa halalcinsa ya fara zagwanyewa.
Turkiyya ta bayar da mafaka ga ‘yan kasar Sham su fiye da dubu 10 a wasu tantunan da ta kakkafa a kusa da bakin iyakarsu.