Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin gwanatin Syria sun kai sumame wani gari dake kusa da kan iyakar kasar da kasar Turkiya


Camp for Syrian refugees on border with Turkey.
Camp for Syrian refugees on border with Turkey.

Sojojin gwamnatin Syria tare da tankokin yaki, sun kutsa wani gari dake kusa da kan iyakar kasar da Turkiya a yau asabar. Sojojin sunyi ta harbi suka kuma kama akalla mutane saba'in.

Masu hankoron kare yancin jama’a a kasar Syria sunce a yau asabar sojojin gwamnati suka kai sumame wani kauye dake kusa da kan iyakar kasar da Turkiya suka yi ta harbi da bindigogi masu sarafa kansu, suka kuma kama wasu mutane.

A yau asabar sojojin dake biyaya ga shugaba Bashar Al Assad suka kutsa garin Badama da akalla tankoki shidda da manyan motocin yaki guda goma da wasu motocin soja. Shedun gani da ido sunce an kama akalla mazauna garin su saba’in, kuma yan bindiga sun cinawa wasu gidaje biyu wuta. Shi dai wannan gari na Bdama bashi da nisa daga kan iyakar kasar da Turkiya.

Wani jami’in wata kungiyar lura da cibiyarta ke birnin London ya fada cewa mazauna wannan gari suna taimakon yan gudun hijira wadanda suka arce kafin su tsalaka zuwa Turkiya.

Yanzu haka dai fiye da yan gudun hijirar Syria dubu goma ne suke zaune a cikin tantunan da aka kakkafa. Yawancin su sun gudo ne daga garuruwan da sojojin gwamnati suka auna. Syria ta kai harin na baya bayan nan ne a yayinda Amirka tace tana nazarin ko ta caji shugaba Assad da laifin aikata laifuffukan yaki ko kuma a’a, a zaman wani bangare na yunkurin diplomasiya da ake yi na ganin gwamnatin sa ta kawo karshen sumamen da take kaiwa yan tawaye ko kuma bijirarru.

Kalli: Video footage of crackdown on protesters June 17, 2011

XS
SM
MD
LG