Manyan shugabannin ‘yan Khmer Rouge da suka rage da ransu sun bayyana yau litinin a gaban wata kotun kasar Cambodia, a lokacin da aka fara shari’arsu da aka jima ana jira bisa zargin cin zarafin bil Adama. Wannan shari’a ita ce muhimmiya a gaban kotun bin kadin laifuffukan yaki a Cambodia wadda MDD take goyon baya, wadda kuma akan kafa domin tabbatar da an yi shari’ar adalci tare da kokarin hada kan kasar wadda ta dade kawunanta na rarrabe a saboda katobarar da ake zargin ‘yan Khmer Rouge da aikatawa a karshen shekarun 1970. Mutane kimanin 500, da yawa daga cikinsu wadanda suka sha azaba a hannun ‘yan Khmer Rouge, sun cika zauren kotun a lokacin fara wannan shari’a. Mutane 4 da ake tuhuma, dukkansu tsoffi, sun zauna a bayan wani kyalle cikin kotun domin jin irin laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa. Daga bisani an kyale uku sun bar kotun saboda ba su cikin koshin lafiya. Wadanda aka gurfanar a yau sune shugaban kasa na ‘yan Khmer Rouge Khieu Samphan mai shekaru 79 da haihuwa; da shugaban akida na kungiyar, Nuon Chea mai shekaru 84 da haihuwa; da ministan harkokin wajensu Leng Sary mai shekaru 85 da haihuwa da kuma matarsa Leng Thirith mai shekaru 79 da haihuwa wadda ita ce ministar kula da kyautata rayuwa ta Khmer Rouge. Shugaban Khmer Rouge na asali, Pol Pot, ya mutu a shekarar 1998.
Manyan shugabannin ‘yan Khmer Rouge da suka rage da ransu sun bayyana yau litinin a gaban wata kotun kasar Cambodia, a lokacin da aka fara shari’arsu da aka jima ana jira bisa zargin cin zarafin bil Adama.