Sakataren tsaron Amurka, Robert Gates, yace takunkumin da aka sanya ma Iran a kan shirinta na nukiliya yana janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin shugabannin kasar, kuma shi ne hanya mafi nagarta wajen lallashin kasar ta watsar da shirin nata.
Wakilin Muryar Amurka a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Al Pessin, ya ambaci sakatare Gates yana fadin cewa shugabannin Iran sun yi mamakin yadda duniya ta rungumi takunkumin, da kuma irin illar da yake yi ma kasar.
Gates ya fadawa gungun shugabannin kamfanonin da jaridar Wall Street Journal ta dauki nauyin tarawa cewa takunkumin yana janyo matsala a tsakanin shugaba Mahmoud Ahmadinejad da shugaban addini na kasar Ayatollah Ali Khameini. Yace, "Wadannan matakan sun yi illa ma kasar fiye da yadda suka zata. Har ma mun fara samun shaidar cewa Khameini ya fara tunanin ko Ahmadinejad yana shara masa karya ce a kan illar da takunkumin yayi ga tattalin arzikin kasar."
Sakatare Gates yace yayi imani shugabannin Iran sun kuduri aniyar kera makaman nukiliya, zargin da suka musanta. Gates yace hanyar warware wannan matsala ta lokaci mai tsawo ita ce ta yin amfani da takunkumi da kuma kafofin diflomasiyya wajen shawo kan ‘yan Iran su fahimci cewa kera makaman nukiliya ba zai biya muradunsu ba.
Sakataren tsaron na Amurka, ya kara da cewa, "Duk wata hanyar dabam (ba ta diflomasiyya ko takunkumi ba) ta wucin gadi ce kawai, wadda amfaninta ba zai shige shekaru biyu ko uku ba. Ni a gani na daukar matakin soja a kan Iran zai janyo hadin kan kasar dake rarrabe a yanzu ne kawai, kuma wannan zai sa kasar ta Iran ta yanke shawarar cewa ko ana ha maza ha mata sai ta mallaki makaman nukiliya, kuma zata kara boye shirin nata ta yadda zai yi wuya a gano shi."
Duk da haka Gates da wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka ba su kawar da yiwuwar daukar matakin sojan ba. A makon jiya ma, firayim ministan bani Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yace tilas ne kasashen yammaci su tabbatarwa da shugabannin Iran cewa a shirye suke su kai ma kasar harin soja idan ba su yarda sun yi watsi da shirinsu na nukiliya ba.