Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Ghana domin kai ziyarar aiki ta wuni guda.
Buhari ya sauka a filin tashin jirage na Kotoka da misalin karfe 10 na safe agogon Ghana, inda aka karrama shi da ala'dar kewaya dakarun kasar.
Shugaba Buhari ya samu tarbar takwaran aikinsa, John Dramani Mahama, wanda zai gana da shi kan huldar kasuwanci da wasu batutuwa da dama.
Baya ga haka dumbin ‘yan Najeriya mazauna kasar suma sun tarbi shugaba Buhari wanda ke sanye da babbar riga.
Tuni rahotanni suka ce ashugabannin biyu sun fara tattaunawa a Fadar shugaban kasar Ghana ta Peduase.
Wasu ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan ziyara inda wasu suka nuna farin ciki yayin da wasu kuma suka nuna rashin gamsuwarsu kan wannan ziyara, kamar yadda za ku ji a sautin da ke kasan wannan rahoto.