Daya daga cikin wadanda suka kasance a wurin taron shi ne Jelani Aliyu shahararen injiyia mai kira wa kamfanin General Motors ko GM motaci a nan Amurka.
A firar da yayi da Aliyu Mustaphan Sokoto ya bayyana irin abubuwan da suka tattauna a taron da kuma tasirin da taron ya yi.
Yace taron yana da anfani sosai saboda sun tattauna akan cigaban kasar. Sun duba abubuwa kaman fannonin ilimi.da kiwon lafiya da kuma ilimin kimiya da fasaha.
Jelani Aliyu yace shi ya bada kasida akan ilimi da cigaban matasa. Yace yakamata a samu makarantu da zasu taimakawa matasa a ilimin kimiya da sana'o'i saboda matasa su daina dogara ga gwamnati. Yanayin yanzu bashi da taimako a ce idan matashi ya gama makaranta sai ya nemi aiki da gwamnati. Kamata ya yi ya samu abun yi balallai sai gwamnati ta bashi wani abun yi ba.
Jelani yana da karfin gwiwar cewa shawarwarin da suka bayar zasu yi tasiri a karkashin sabuwar gwamnatin Buhari ba yadda aka saba gani ba saboda wakilan gwamnati a taron sun yi na'am da shawarwarin..
Dangane da yunkurin wasu kamfanonin Amurka dake son zuwa Najeriya su fara kera motoci, Jelani yace yunkurin nada kyau domin motocin Amurka nada karfi sosai. Jelani bai yadda cewa motocin kasar Japan sun fi na Amurka karfi ba.
Wani shiri da Najeriya ta fitar dashi a karkashin gwamnatin da ta shude, Jelani yace zai baiwa masu son kera motoci a kasar karfin gwiwa. Saidai abu mafi dacewa shi ne a samu 'yan Najeriya suna kirkiro motocin ba a kawo masu a hadasu ba kawai.
Ga karin bayani.