Najeriya na cikin kasashen Afirka da 'yan kasar suka yi kamarin suna wajen kin biyan haraji ga gwamnati.
Galibin 'yan kasar ba kasafai suke mutunta dokokin biyan haraji ba. Kalilan din dake biya sun bayyana rashin gamsuwarsu musamman akan yadda hukumomin kasar ke sarafa kudaden harajin.
Wasu sun ce duk wata suna biyan haraji da suka hada da na kananan hukumomi da na jiha.
Masu biyan harajin sun amince dole ne kuma suna biya saboda suna sa rai za'a yi masu aiki da kudaden da suke biya.
Duk da biyan jama'a da dama suna da bukace bukace. Misali a wasu unguwannin sai a dauke ruwan fanfo sati daya ko biyu basu samu ruwa ba.
Wasu suna biyan kudin harajin ne saboda basa son a damesu ba wai sun gamsu ba ne. Idan basu biya ba za'a dinga binsu kullum tamkar suna bin bashi. To saida basa ganin aikin da a keyi masu.
Bincike ya nuna bayan rashin karfin gwiwa da masu biyan ke dashi hukumomi ma basu da sahihin tsarin biyan haraji.
Wani masani Malam Habu Ahmed yana cikin masu sharhi akan al'amuran yau da kullum. Yace ba za'a ce mutane su dinga biyan haraji ba sai an san yawan wadanda suka cancanta su biya harajin. Haka kuma a san yawan arzikin da suke samu kana a kiyasta adadin kudaden da ake son a samu daga wurinsu. Sai kuma a samo hanya mafi sauki da mutane zasu biya harajin.
Bayan an biya haraji to me a keyi da kudaden. Mutane suna bukatan cikakkun bayanai a rubuce, cikakkun bayanai a fili da kuma cikakkun bayanai a aikace.
Ga rahoton Ibrahim Mahmud Kwari.