Wanda ya taimaka wajen dakile tashe-tashen hankulan da aka kwashe fiye da shekara guda ana fama da su, yana mai cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen rikicin.
A daren jiya shirin tsagaita wutar ya fara aiki wanda aka cimma da gwamnatin Yamal, da dakarun da Saudiyya ke jagoranta da kuma ‘yan tawaye Houthi da suka karbe ikon babbanin birnin Yamal a farkon shekara ta 2014, dukkaninsu kuma sun amince da wannan shiri na tsagaita wuta.
Wannan shirin na zuwa ne gabanin wani taron sasanta rikicin na Yamal da za a yi ranar 18 ga watan nan na Afrilu a kasar Kuwait.
Ahmed ya kara da cewa, har yanzu akwai kofar da za a iya sake farfado da kasar, wacce ta sha fama da rikici na wani tsawon lokaci da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu shida.