Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin tsagaita wuta a yakin Syria ya shiga yini na uku


Babban sakataren MDD Ban Ki-moon yace shirin tsagaita wuta a Syria na cigaba duk da wasu matsaloli
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon yace shirin tsagaita wuta a Syria na cigaba duk da wasu matsaloli

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya ce, duk da wasu ‘yan tashe-tashen hankula da aka fusakanta, shirin tsagaita wutar da aka cimma ya shiga yini na uku.

Mr Ban ya kara da cewa yanzu haka wata runduna ta musamman na sa ido a shirin tsagaita wutar, domin kada a samu bazuwar tashin hankali da aka samu a wasu wurare.

Ministan harkokkin wajen Faransa Jean- Marc Ayrault, ya kira wani taron gaggawa, domin tattaunawa kan yankunan ‘yan tawaye da aka ce an kai ma hare-hare.

A ranar Asabar din da ta gabata, shirin tsagaita wutar ya fara aiki, inda aka samu korafe-korafen cewa duk bangarorin da suka amince sun keta dokar shirin na tsagaita wuta.

Su dai bangaren ‘yan adawa sun yi korafin cewa dakarun Bashar al Assad sun kai hare-hare a wasu garuruwa da ke hannunsu.

Wasu fararen hula suna gyara bututun ruwa da aka lalata lokacin yaki da yanzu ana iya gyarawa saboda tsagaita wuta
Wasu fararen hula suna gyara bututun ruwa da aka lalata lokacin yaki da yanzu ana iya gyarawa saboda tsagaita wuta

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG