Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Mika Mulki: Buhari Ya Koma "Glass House" Da Zama


Shugaba Buhari (Facebook/Femi Adesina)
Shugaba Buhari (Facebook/Femi Adesina)

"A yau na zagaya da uwargidan zababben shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu fadar shugaban kasa don ta ga zubin fadar." In ji Aisha.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kaura zuwa wani sashe na Fadar Shugaban kasa da ake kira “Glass House.”

Uwargidan shugaban Aisha Buhari ce ta bayyana hakan a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram, wanda ya nuna yadda ta tarbi uwargidan zababben shugaban kasa Sanata Oluremi Tinub inda ta zagaya da ita fadar shugaban kasar.

"A yau na zagaya da uwargidan zababben shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu fadar shugaban kasa don ta ga zubin fadar.

“Yanzu mu muna zaune ne a Glass House. Mu biyu ne kadai da mijini a cikin gidan.” Aisha ta ce.

Bisa ala’da, wannan sashe na “Glass House,” shi ne bangaren da Shugaba mai barin gado ya kan zauna yayin da ya rage kwanaki kafin ya sauka a mulki.

Aisha ta kara da cewa, ya kamata a ci gaba da dabbaka wannan al’ada ta ajiye shugaban kasa mai barin gado a wanna gida.

“Mun gode Allah da ya nuna mana karshen wa’adin mulkinmu." Aisha ta ce a bidiyon mai tsawon minti daya da dakika 20.

A ranar 29 ga watan Mayu Buhari zai mika mulki ga Ahmed Bola Tinubu wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairu, ko da yake, 'yan adawa na kalubalantar sakamakon a kotu.

XS
SM
MD
LG