An samu mabambantan ra’ayoyi kan bukatar Shugaba Buhari ga jama’a, wadanda su ke ganin ya yi mu su laifi da su yafe ma sa. Hakika tun bayyanar wannan labari na neman afuwa wasu ke cewa Allah ya yafe wa kowa yayin da wasu ke mamakin neman afuwar da ya yi don su na daukar shugaban a amtsayin wanda ba ya nadamar duk matakan da gwamnatinsa ta dauka, kazalika ya kan toshe kunne daga duk korafe-korafen da jama’a ke yi.
Ga irin su dattijo Hussaini Gariko da ya sha fafukar dan arewa ya zauna kan mulki, ya ce gaskiya ‘yan arewa in ka debe ‘yan jari hujja ba su amfana da mulkin Shugaba Buhari ba.
Shi kuma kakakin Sarkin Keffi a jihar Nasarawa, Yahaya Shafale, ya tuno wahalar da mutane su ka sha ne wajen canjin kudin da ba a canja ba inda karshe a ka dawo amfani da tsoffin kudi bayan mutane sun galabaita.
Masu wa’azi irin Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe sun yi wa shugaban fatan alheri da neman yafewar ubangiji.
Shugaba Buhari dai wanda bai faye zantawa da manema labaru ba tun hayewar sa karaga a 2015 ya sha alwashin mutane za su gani a kasa.
Buhari ya ce lokaci ya yi da zai yi bankwana da mazauna Abuja zuwa mahaifarsa kuma zai yi nesa da su ne ba wai don wata damuwa ba don ya yaba wa kauna da su ka nuna masa, amma ya na ganin ya dace ya sulale zuwa ritaya. A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya: