Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saura Kasa Da Wata Guda Buhari Ya Mika Mulki


Shugaba Buhari (Hoto: Facebook/Femi Adesina)
Shugaba Buhari (Hoto: Facebook/Femi Adesina)

Buhari ya sha nuna zakuwarsa ta ganin ya mika mulkin kasar ga sabuwar gwamnati.

Yau Asabar 29 ga watan Afrilun 2023, kwana 30 cur suka rage shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika mulki ga sabuwar gwamnati.

A ranar Litinin 29 ga watan Mayu, Buhari wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu zai mika mulki ga sabuwar gwamnati karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu ne ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairu karkashin jam’iyyar APC mai mulki – ko da yake, jami’yyun adawa na kalubalantar sakamakon zaben a kotu.

A makon da ya gabata Buhari ya bayyana cewa ba-gudu-ba-ja-da-baya a shirinsa mika mulki a ranar 29 ga watan na Mayu.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne yayin da yake gaisuwar Sallah da Tinubu ta wayar tarho kamar yadda rahotanni suka nuna.

Tun gabanin hakan ma, Buhari, wanda ya bayyana zai koma mahaifarsa ta Daura da ke jihar Katsina da zama, ya sha nuna zakuwarsa ta ganin ya mika mulki.

A lokacin da yake karbar gaisuwar Sllah a fadarsa a makon da ya gabata, Buhari ya nemi afuwar "wadanda ya yi wa ba daidai ba."

A makon da ya gabata Tinubu ya koma Najeriya daga turai bayan da ya yi balaguron sama da wata daya.

XS
SM
MD
LG