A jiya Talata Kwamitin ya umurci sojojin ruwa na kungiyar tarayyar turai da su dakatar da duk wani jirgin ruwa da zai shiga ko fita a kasar ta Libya domin yi masa binciken kwakwaf, kuma su kwace duk makaman da suka gani wanda zai shiga kasar ba bisa kaida ba.
Wannan matakin dai zai fadada aikin kungiyar tarayyar Turai da take yi a wannan yankin wanda tun a shekarun baya ne take kokarin ganin ta hana fasa kwabrin da akeyi ta tekun medetereniyan.
Jakadan Faransa a kungiyar Francois Delatre wanda shi ne ya gabatar da wannan kudirin a wajen taron, yace ba shakka wannan zai shawo kan matsalar tsaro da kuma canjin yanayi a kasar ta Libya.
Yace suna sane da cewa kaucewa dokar mallakar makamai ba abinda yake haifar wa sai karin rashin zaman lafiya da kuma karfafa harkokin kungiyar Daesh ko ISIS wadda take babbar abokiyar gabar kungiyar ce ta tarayyar Turai.
Yanzu haka dai wannan matakin ya umurci sojojin ruwan su binciki duk wani jirgin ruwan da ya shigo cikin ruwar kasar, kuma muddin suka samu makamai ko wani abu mai kama da haka wanda ya karya dokokin mallakar makamai to sojojin su kwace su kana su karkata akalar jirgin da matukan sa a duk tashar jirgin da ya dace akai jirgin.