Libya ta dare gida 2 tsakanin kungiyoyi masu gaba da juna: gwamnatin hadin kan kasa da al’ummar kasa da kasa suka amince da ita, mai mazauni a birnin Tripoli, da kuma gwamnatin samar da daidaito a kasa, mai samun goyon bayan Majalisar Wakilai da rundunar sojan kasar, dake iko da rabin kasar ta gabashi.
Rigimar dake tsakanin kungiyoyin 2 masu gaba da juna ba ta waye zai shugabanci kasar bane. Tafi karkata ne ga waye zai mallake kudaden shigar kasar daga cinikin fitar da danyen mai.
Tabbas, fasa kwabrin man fetur babbar matsala ce a Libya, wacce ta karu tun bayan faduwar gwamnatin gaddafi.
Duk da haka, duk da takaddamar siyasar, ko kuma mai yiyuwa saboda ita, Libya ta samu dan daidaiton al’amura tsawon shekaru 3.
Sai dai, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, “bambance-bambancen da suka jima a zukatan mutane da wadaka da tattalin arzikin kasa da ci gaba da tauye hakkokin dan adam da muradai daga ciki da wajen kasar masu cin karo da juna, na ci gaba da rauzaye hadin kai da samun daidaito a kasar” yake kara cusa kasar cikin hatsarin fadawa cikin sabon rikici.
“Maslahar siyasa ce hanyar samun daidato al’amura a Libya,” a cewar Dorothy Shea, jakadiyar Amurka kuma ta Majalisar Dinkin Duniya a mataki na wucin gadi a Libya. “lokaci na da matukar mahimmanci a kokarin da Majalisar Dinkin Duniyar ke jagorantar duba da kokarin da wasu daga wajen kasar ke yi na wargaza ta.”
“Muhimmin al’amari kan kare diyauci da martabar yankunan Libya shine sake hade hukumomin kasar a wuri guda ta hanyar hade harkar tsaron yankunan gabashi da yammacinta, wanda yanzu za’a iya amincewa dashi sakamakon sauye-sauyen da majalisar tayi kam batun takunkumin makamai a watan daya gabata.”
Jakadiya Shea ta yi jan hankalin cewa “muhimman abu kan dorewar yarjejeniyar tsagaita wutar Libya da kuma cimma burin sake hade kasar na kunshe a cikin kudurorin majalisar da zasu biyo baya.”
“Domin dorawa a kan wannan cigaban da aka samu, muna kira ga bangarorin dake rikici da juna a Libya su cimma yarjejeniya akan hadadden kasafin kudin da zai alkinta daidaiton tattalin arzikin kasar, tare da zuba jari a harkokin cigaba da kuma kawo karshen yawan tashin rikici akan rabon kudaden shiga da suka janyo durkushewar kasar a baya.”
A karshe, saboda arzikin Libya na dukkanin al’ummarta ne, ba wai ‘yan tsirarrun dake tasarufi dasu ba, Jakadiya Shea ta jinjinawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar game sabunta rabe-raben mutanen dake gurgunta libya ta hanyar diba da fataucin danyen mai zuwa wajen kasar ta haramtacciyar hanya.
“Satar mai na sanadiyar zurarewar dimbin arziki zuwa wajen Libya,” a cewarta. Domin walwalar al’ummar Libya, wajibi ne a magance wannan matsalar sata da almundahana.”
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.
Dandalin Mu Tattauna