Muryar Amurka ta tuntubi shugaban kungiyar iyayen ‘yan matan Chibok, Yakubu Nkiki, wanda ya tabbatar da cewa yarinyar da aka ceto Sera Lukas, ba yarsu bace domin babu sunan ta cikin kundin sunayen daliban da aka sace.
Shima sakataren kungiyar Lawan Zanna, cewa yayi rundunar sojan Najeriya basu tuntubi iyayen yaran ba domin tabbatarwa kafin fitar da rahotan cewa Serah Lukas, na daga cikin daliban makarantar Chibok. A ranar Talatar da ta gabata ne aka ceto Amina Ali, mai shekaru 19 tare da jaririyarta bayan da ‘yan kato da gora suka kai wani samame a dajin Sambisa da ke jihar Borno. An kuma dauki yarinyar zuwa gidan iyayenta inda suka tabbatar da cewa yar su ce kafin fitar da rahotan.
Lawan Zanna, yayi kira ga rundunar sojan Najeriya, da cewa nan gaba duk yarinyar da aka kwato tace ita yar Chibok ce a fara tuntubar iyayenta ko kungiyarsu kafin a shedawa duniya.
Domin karin bayani.