Gwamnatin jihar ta zargi 'yan kungiyar kwadagon da wuce makadi da rawa.
Gwamnatin ta nuna bacin ranta da tilastawa wasu ma'akata da kuma rufe sakatariar gwamnati.
Kwamishanan yada labarai na jihar Ahmed Sajoh yace gwamnatin ba zata lamunce ba da halin karya doka da jami'an 'yan kwadagon keyi. Yace 'yan kwadago basu da ikon su dinga fatattakar ma'aikata.
Yace kungiyar ta dauki bulala tana dukan mutane. Ganganci ba aikin 'yan kwadago ba ne. Yace sun kulle sakataria wadda kuma ba tasu ba ce. Ta gwamnati ce.
Ya kirasu da su daina koran mutane ko kulle. Gwamnati ba zata taba su ba amma kuma ba zata yadda a kulle mata sakataria ba. Hakin kungiyar kwadago na kan 'ya'yan kungiyar ne kawai. Su yi aiki da hankalin da Allah ya basu.
To saidai a martanin da kungiyar ta bayar ta bakin shugabanta Kwamred Dauda Maina ta musanta zargin tare da cewa gwamnatin jihar na kokarin bata masu suna ne.
Ga karin bayani