Yace abun da ya gani da idanunsa dangane da wahalar rayuwar wadanda tarzomar Boko Haram ta raba da gidajensu na kara ta'azzara.
Mr O'Brien yace tarzomar Boko Haram ta tagayyara kimanin mutane miliyan tara da dubu dari biyu a ksashen yankin tafkin Chadi. Cikin wannan adadin mutane miliyan biyu 'yan Najeriya ne wadanda yanzu sun kwashe fiye da shekaru biyu suna cikin halin kakanikayi.
Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan yace zasu samarda yadda za'a yi hubbasa wajen samarda bukatun jin kai da 'yan gudun hijiran suke tsananin bukata. Yace idan ba'a yi hakan ba to ko babu abun da za'a yi masu a matsayin taimakawa rayuwarsu domin su fita daga halin da suke ciki yanzu.
Babban darakta na hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA Alhaji Sani Sidi yace yanzu da sojojin Najeriya ke gap da kawo karshen yakin Boko Haram, aikin jin kai na sauyawa daga bada agajin gaggawa ya zuwa na maido da wadanda tarzomar ta girgiza cikin hayacinsu.
Alhaji Grema Corop, tsohon shugaban hukumar bada agajin gaggawa a daya daga jihohin arewa maso gabas yace abun da Mr. O'Brien ya ganowa idanunsa su ne suke faruwa a zahiri, kuma ba shi ne ya fara irin maganar da ya yi ba.Shugaban kungiyar ICRC ta duniya gaba daya shi ma ya taba fadan hakan har ma yace a jihar Borno ya ga mutane suna mutuwa sanadiyar yunwa da cututtuka.
Ga karin bayani.