Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, Sepp Blatter, yayi murabus haka kwatsam a yau talata a ganiyar wani abin fallasa na almundahana a hukumar.
Kwanaki hudu kacal da suka shige aka sake zaben Blatter a matsayin shugaban hukumar FIFA. Yayi kiran da a gudanar da taron gaggawa na hukumar kwallon kafar domin zaben wanda zai gaje shi, ya kuma ce zai ci gaba da zama kan kujerar har zuwa lokacin da za a samu wanda zai gaje shi.
Sai dai kuma kila za’a yi watanni kafin a gudanar da zaben sabon shugaban hukumar ta FIFA. Masu kula da sha'anin hukumar ta FIFA sun ce watakila sai a tsakanin watan Disambar wannan shekara zuwa watan Maris na 2016 za a iya gudanar da zaben sabon shugaba.
Shugaban mai shekaru 79 da haihuwa ya bayar da sanarwar shawarar da ya yanke a yau Talata a birnin Zurich. Ko da yake FIFA na fama da maganar zargin da ake ma manyan jami’an na zarmiyya da cin hanci da rashawa, Blatter dai ya wanke hannun sa kan maganar ya kuma ci alwashin maido da mutuncin hukumar da share duk wani ake zarginsa da hannun kan aikata wasu ayyukan rashin gaskiya.