Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiran Amurka Ga Shugaban Kasar Burundi


Ofinshin jakadancin Amirka dake kasar Burundi yace yana ci gaba da kira ga shugaban kasar Pierre Nkurunziza da ya yi watsi da kokarin tsayawa takara a karo na uku, shawarar da ta janyo mumunar zanga-zangar tun lokacinda da shugaban ya bada wannan sanarwar a watan Afirilu.

Ofishin na jakadancin Amirkar dake birnin Bujumbura yace shirin Mr. Nkurunziza ya sabawa yarjejeniyar da ta kawo karshen tarzomar da aka yi shekaru ana yi a kasar, kuma hakan na iya jawo barazana ga samun kwaniciyar hankali daga yakin basasa.

A wani bayani da ofishin jakadancin ya fitar na nunin cewa a yanzu haka babu wani yanayin a kasar Burundi na yin zabe tsakani da Allah, a dalilin kuntatawa ‘yan siyasa da rufe gidan jaridu masu zaman kansu, da yadda gwamnati ke murkushe masu zanga-zangar siyasa, harma da ci gaba da kuntatawa mutanen kasar.

Shugabannin kasashen gabashin Afirka sunyi taro ranar Lahadi inda suka tattauna kan tashin hankalin kasar Burundi, inda sun kuma yi kira shugaba Nkurunziza da ya dakatar da zaben kasar mai zuwa da aka shirya yi 26 ga watan Yuni da akalla makonni shida. A jiya Litinin mai magana da yawun shugaban kasar yace shugaban zai yi nazarin wannan kira. Amma mataimakin mai magana da yawun shugaban Gervais Abayeho, ya fada ma Muryar Amirka cewa duk jinkirin da za’ayi ba zai bai kamata ba ace an nisanta zaben kasar.

Shugaban kasar dai yace yana da ‘yancin tsayawa zabe a karo na uku, saboda ba zabar sa akayi ba a lokacin da ya karbi mulki karon farko, amma masu caccakar sa sunce tsayawa takara karo na uku zai sabawa kudin tsarin mulkin kasar.

XS
SM
MD
LG