Wata kwamishinar zabe ta kasa a Najeriya, Hajiya Amina Zakari, ta ce matsalolin da aka samu na rashin yin zabe a wasu sassan jihar Kogi, sune suka sanya za a sake gudanar da zaben gwamna a wadannan yankunan, ba wai don an samu tashin hankali ko kuma an aikata abubuwan da ba su kamata ba.
A hirar ta da VOA Hausa, Hajiya Amina Zakari, ta ce al'ummar Jihar Kogi da dama sun bayyana cewa an jima ba a gudanar da zaben da ya tafi sumul kamar wannan ba.
Ta ce rashin tsaron da aka samu a wasu sassan suka sanya ba a gudanar da zabe ba, amma yanzu da yake an tabbatar wannan zabe na gwamna bai kaya ba, tilas a sake zabe a wadannan wuraren domin a san abinda al'ummar jihar suke bukata.
da take magana kan rasuwar dan takarar gwamnan jam'iyyar APC, Prince Abubakar Audu, tun kafin a bayyana sakamakon wannan zabe, Hajiya Amina ta ce tsarin mulki bai bayyana yadda za a yi idan haka ya faru ba.
Haka ma dokokin zabe na kasa ba su ce ga yadda za a yi ba.
Dalili ke nan da ya sa hukumar INEC ta ba jam'iyyar da ta tsayar da wannan dan takara, sukunin sake mika sunan wani dan takarar da zai maye gurbin wanda ya rasu.
Jam'iyyar PDP dai ta ce ba ta yarda da wannan matsayi da hukumar zaben ta INEC ta dauka ba, yayin da ita INEC din take cewa jam'iytyar tana iya shiga kotu idan ba ta gamsu da wannan matakin ba.