Babban bankin Najeriya ko CBN a takaice ya rage kudin ruwan da yake karba daga bankuna daga kaso 13 zuwa kaso 11 cikin dari.
Da ma bankunan kasuwanci daga babban bankin kasar suke karbar lamuni domin su cigaba da ayyukansu na sayar da kudi wato ba 'yan kasuwa da masana'antu bashi su cigaba da hada-hadar tattalin arziki.
Kakakin bankin yace abun da bankin ya yi yana cikin hanyoyin da bankin ke dauka domin habaka kasuwanci da bunkasa tattalin arzikin kasa. Rage tsadar kudi da 'yan kasuwa ke ranta zai taimaka.
Ta bakin kakakin babban bankin baya takurawa bankunan kasuwanci saboda bankin yana nazari akan yawan kudin da ake juyawa a kasuwar kasa. Idan kudi ya yi yawa ainun zai gurbata tattalin arziki. Idan kuma an samu karancin kudi shi ma zai gurbata tattalin arziki. Aikin babban bankin ne ya tabbatar babu yawa babu karancin kudi a harkokin kasuwanci kasa.
Yushau Aliyu wani kwararre akan tattalin arziki yace rage kudin ruwa wani abu ne da sun dade suna kiran babban banki ya yi domin ya taimakawa masu karamin karfi su aro kudade daga bankuna domin su koma harkokin kasuwanci gadangadan. Tsdar kudi na hana 'yan kasuwa masu karamin karfi neman aro lamarin da ka hana habaka kasuwanci da kuma kara daukan ma'aikata.
Ga karin bayani.