Hare-haren Adamawa da Kano sun sa masana harkokin tsaro suna kiran jama'a da su kara daukan matakan tsaro domin rage yawan barnar da hare-haren kan haddasa.
Halin ko in kula da jama'a ke nunawa a kan sha'anin tsaro shi yake ba 'yan ta'ada damar kaddamar da hare-haren. Saboda haka aka kira jama'a da su kula wajen fannin tsaron kai da kai domin rage hare-hare..
Dangane da wuraren ibada irin su masallatai da mijami'u masana harkokin tsaro sun kira jama'a da su tsaurara matakan tsaro banda wanda hukuma ke yi. Su lura da kasuwanni da tashoshin motoci da makarantu.
Kanal Isa Gwani ritaya ya shawaraci jama'a cewa duk inda aka dauki matakan tsaro to kada a yi sakaci. A cije a cigaba a kuma yi hakuri. A yi anfani da 'yansanda su horas da jama'a akan harkokin tsaro domin su taimaka.
Alhaji Adamu Maigala ma fashin bakin alamuran yau da kullum ya bukaci al'umma da su tashi kai tsaye kan batun tsaron kai da kai. Yace gwamnati ta ci karfin 'yan ta'adan dalili ke nan suka canza salo suna shiga cikin jama'a. Yace babu yadda za'a shawo kansu sai jama'a sun sa ido kan kowa. Jama'a su lura da kansu. Su dinga daukan matakan kare kai. Su kula da masallatai da coci-coci da kasuwanni da duk wurin taron jama'a.
Ga karin bayani.