Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Kai Ziyarar Neman Hadin Kai Kasar Rasha


A yayin da ake ci gaba da fafatawa da yaki da ta'addanci da kungiyoyin 'yan ta'adda irin su ISIS, da al-ka'ida da sauran su, Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya kai ziyara birnin Moscow a wani yinkuri na neman hadin kan Rasha kan yaki da ta'addanci a Siriya.

Duk kuwa da tsamin dangantaka tsakanin Amurka da Rasha kan batun Ukrain da NATO da kuma wasu batutuwan, wanda ya sa kowane bangaren ke nuna rashin yadda da dayan.

Tattaunawar ta tsawon kwanaki biyu da Skataren Harkokin Wajen na Amurka zai yi da Rashawan, za su shafi batutuwa da dama; to amma wasu bayanai da aka kwarmato, wadanda aka fara bugawa a jaridar Washington Post, na nuna cewa Kerry zai yi ma Shugaban Rasha Vladimir Putin tayin wani tsari na hadin gwiwar soji tsakanin Rasha da Amurka a yaki da ISIS, da al-Ka'ida da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a Siriya.

Kafin ya kama hanyar Moscow, Kerry ya ki ya yi cikakken bayani, to amma ya tabbatar cewa zai gana da Shugaba Putin da mukarrabinsa a Kremlin, Sergei Lavrov.

Haza zalika, jami'ai a Kremlin ba su ba da cikakken bayani ba.

"Mu na sa ran ziyarar da Kerry ke yi a Rasha za ta taimaka wajen kyautata halin da dangantaka tsakanin Amurka da Rasha ke ciki, ganin cewa tabbatar da kwanciyar hankali a duniya da kuma warware takaddama iri-iri a duniya ta dogara ne kansu," a cewar Ministan Harkokin Wajen Rasha jiya Alhamis.

XS
SM
MD
LG