Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Laraba Bam da Ya Tarwatse Ya Kashe Mutane Takwas A Iraqi


Motar da dan kunar bakin wake ya tarwatsa da bam yau Laraba a kasar Iraqi
Motar da dan kunar bakin wake ya tarwatsa da bam yau Laraba a kasar Iraqi

A kalla mutane takwas aka kashe, goma sha daya kuma suka ji rauni yau Laraba bayanda wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa motarsa a wajenda ‘yan sanda ke binciken ababawan hawa a arewacin Babagaza, bisa ga cewar jami’an ‘yan sandan Iraq, kwana daya bayanda aka kai irin wannan kazamin harin da aka yi asarar rayuka a lardin.

Rahotanni na nuni da cewa, dan kunar bakin waken ya rafka motarsa dake dankare da nakiya a wurin binciken ababan hawan dake lardin al-Rashidiya, arewa maso gabashin kasar, unguwar da galibi mazauna‘yan Shi’a ne. Kungiyar ISIS ta fitar da sanarwa jim kadan bayan harin, inda ta dauki alhakin harin kunar bakin waken.

A harin da aka kai jiya Talata, a kalla mutane goma sha biyu aka kashe bayanda wani dan kunar bakin wake a cikin mota, ya tarwatsa kansa kusa da wata kasuwar sayar da kayan marmari da ake samun cunkoson jama’a. Ala tilas ‘Yan sanda suka killace manyan hanyoyin kewayen Bagadaza biyo bayan harin.

A cikin hare hare biyu da aka kai makon da ya gabata, ISIS ta kashe sama da mutane dari uku. A harin na farko, wata motar dakon kaya ta tarwatse a wani wurin hada hadar kasuwanci a wata unguwar ‘yan Shi’a da ake kira Karada. Tare da kisan mutane dari biyu da casa’in da biyu, hare haren sun kasance mafiya muni a Iraq da aka yi asarar rayuka tun shekara ta dubu biyu da uku da Amurka ta kai mamaya. A wani harin kuma ranar alhamis, an kashe mutane 37 a wani hari da ‘yan Shi’a suka kai a wani dakin ibada dake arewacin Bagadaza.

Kungiyar ISIS tana zafafa kai hare hare kwanan nan, abinda ya sa sakataren tsaron Amurka Ash Carter a farkon wannan makon, yace za a tura Karin dakarun Amurka dari biyar da sittin Iraq domin su taimaka a yaki da kungiyar ta’addancin.

XS
SM
MD
LG