Sabuwar Firayim ministar 'yar shekaru 59 ana kyautata zaton nan ba da dadewa ba zata bayyana ministocinta da zasu hada da ministan da zai kula da ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai.
A jawabinta na farko a matsayinta ta zama Firayim Minita, May tace ta kuduri aniyar jan ragamar mulkin kasar cikin hadin kai ta yadda zata gina kasar da "kowa zai anfana" Tace zata yaki rashin adalci kuma ta tsaya kan hadin kan duk 'yan Birtaniya.
Tace "zamu shawo kan duk wani kalubale. Yayinda da muke barin Kungiyar Tarayyar Turai, zamu cigaba gabagadi mu samar ma kanmu sabuwar rawar da zamu taka a duniya. Zamu tabbata Birtaniya ta kasance kasar kowa ce ba ta wasu kalilan ba", inji May.
Ta cigaba da cewa "gwamnatin da zan jagoranta ba zata kare muradun wasu kalilan ba kawai amma na kowa da kowa. Zamu yi duk iyakacin kokarinmu mu baku iko akan harkokinku.
Kodayake sabuwar Firayim Ministar bata goyi bayan ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai ba amma tace "ficewa na nufin ficewa". Sai dai kuma ta jaddada bukatar dake akwai a samu daidaituwa kan ficewar daga kungiyar Tarayyar Turai ta yadda Birtaniya zata samu alfanu.