A toron manema labarai da Ma'aikatar Harkokin Wajen ta kira jiya Talata, mukaddashin kakakin Ma'aikatar Mark Toner, ya amsa tambayoyi da dama na manema labarai game da taron na NATO.
Daya daga cikin manema labaran ya ce an gaya masa cewa NATO ta yi ma Tillerson, tayin ranaku daban-daban na gudanar da taron don ya samu damar zuwa, amma Toner, ya karyata wannan. Ya ce matsalar na da nasaba da yadda takaddama kan lokacin taron.
"Mu na masu nuna godiya saboda da kokarin da aka yi na ganin Sakatare Tillerson, ya samu halartar taron. Zan iya tabbatar ma ku cewa mun yi tayin ranaku daban-daban da kowane daya daga cikinsu aka zaba, Sakatare Tillerson, zai iya zuwa, kuma yanzu haka ana kan nazarinsu.
Amma kuma ya kamata a fahimci cewa ba hedikwatar NATO ce kadai ke da hurumin yanke hukunci akai ba, a wannan marrar sai kasashe 28 sun cimma jituwa a kai."
Wani jami'in Ma'aikatar Harkokin Wajen kuma ya ce Tillerson, zai je kasar Italiya a watan Afirilu don halartar taron G-7, daga nan kuma ya wuce zuwa Rasha.
Facebook Forum