A yau Litini shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da batun dake fadin cewar ya hada kai da Rasha don ta taimaka masa ya lashe zaben kasar abun da yace wani uziri ne yan jami’iyar Democrat suke bayarwa na faduwar zabe.
A sakwanni da ya dora a kan shafinsa na tweeter, Trump yace darektan ma’aikatar leken asiri James Clapper a karkashin shugabancin Barack Obama da sauransu sun ce babu wata shaida cewar ya hada kai da Rasha don su taimakawa muradunsa. Trump yace wannan duk labarai ne na karya kuma kowa ya san da hakan.
Watanni biyu da Trump ya dere a kan shugabancin kasar, yace yan jami’iyar Democrat suna kokarin labewa da zancen Rasha don su bada uziri a kan gagarumin rashin nasara da suka yi. Ya kara da cewar kwamitin yakin neman zabe na tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ya dauka cewar zai yi nasara a zabe amma duk da haka suka sha kashi.
Kalaman na Trump da ya yi a baya bayannan na zuwa sa’o’i kadan kafin kwamitin harkokin tattara bayanan sirri na majalisar wakilan kasar ya fara sauraren jawaban shaida daga wasu manyan jami’an Amurka guda biyu a kan bincike da sashen tattara bayanan sirri na kasar suka gudanar a kan zargin Rasha ta yi katsalanda a a zaben kasar don taimakawa Trump ya lashe zaben. Kana a gano ko akwai kanshin gaskiya game da zargi mai daga hankali wanda babu babu shaida, da ya yiwa tsohon shugaba Obama cewar ya yi kutsen wayoyiyn gidansa na Trump Towers a birnin New York.
Facebook Forum