Jami'in ya bayyana cewa hukumar tasa na binciken yiwuwar alaka tsakanin Kwamitin yakin neman zaben Trump, da kasar Rasha.
Haka zalika, a zaman Majalisar da ta gabata, da kyar 'yan Majalisar Wakilai na jam'iyyar Republican, su ka ambaci fitowa karara da Comey ya yi, na yin watsi da zargin da Trump, ya yi cewa tsohon Shugaban Barack Obama ya yi ta tatsar bayanai game da shi a yayin zaben 2016.
Haka kuma sun ki cewa wani abu akai ko a yayin da su ka tashi daga wata ganawa da Shugaba Donald Trump, wanda ke kokarin zawarcinsu don samun isasshen kuri'u na amincewa da sabon kudurin doka na shafewa da kuma maye gurbin Dokar Saukake ma majinyaci samun lafiya wadda aka fi sani da Obamacare.
"Da gaske ka ke yi kuwa?" abinda dan Majalisar Wakilai Walter Jones, dan jam'iyyar Republican daga North Carolina, ya fada kenan bayan da aka tambaye shi ko shin Shugaban kasa ya tabo batun zargin na tatsar bayanai a yayin ganawarsu gabanin kuri'ar da za a kada kan saukaka jinya din ranar Alhamis.
Facebook Forum