Rundunar sojin Najeriya ta kara jaddada cewa, tana kan bincike kan rahotanni da ke nuna mai yiwuwa an kashe shugaban kungiyar Boko Haram ko kuma ya ji mummunan rauni yayin wani gumurzu da aka yi da wata kishiyar kungiyar.
Kakakin sojin kasar Mohammed Yerima ne ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters hakan a ranar Juma’a.
“Jita-jita ce. Muna kan bincike. Ba za mu iya cewa komai ba sai mun tabbatar da aukuwar hakan,” In ji Yerima.
Rahotanni da dama da kafafen yada labaran Najeriya suka wallafa a ranar Alhamis, sun ruwaito wasu majiyoyi na tattara bayanan sirri, wadanda suka ce an ji wa Abubakar Shekau mummunan rauni ko kuma an kashe shi yayin wata arangama da ‘ya’yan kungiyar ISWAP.
Kamfanin Reuters ya ce bai tabbatar da wannan labarin a gashin kansa ba.
A shekarar 2016 ISWAP ta balle daga kungiyar ta Boko Haram.
Karin bayani akan: ISWAP, Boko Haram, Abubakar Shekau, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Abubakar Shekau, ya kasance madugun kungiyar ta Boko Haram mai ikirarin jihadi, wacce ta faro daga shekarar 2009.
Hare-harenta sun yi sanadin mutuwar sama da mutum 30,000, sun kuma raba mutum miliyan 2 da muhallansu, abin da ya haifar da daya daga yanayi mafi muni da ya jefa jama’a cikin halin kuncin rayuwa a duniya.