Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Da Gaske An Kashe Abubakar Shekau? 


Abubakara Shekau / AFP PHOTO / BOKO HARAM AND AFP PHOTO / HO
Abubakara Shekau / AFP PHOTO / BOKO HARAM AND AFP PHOTO / HO

Masu sharhi kan al’amuran tsaro da bincike kan ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda irinsu Barrister Bulama Bukarti sun ce, suna bin diddigin rahotannin da ke nuna cewa an kashe Shekau.

Rahotannin kafafen yada labaran Najeriya na cewa an kashe shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

Bayanai sun yi nuni da cewa Shekau ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da wata arangama da ‘ya’yan kungiyar kungiyar ISWAP ta kaure.

Bisa wasu bayanan sirri da ta samu, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da yammacin ranar Laraba aka kashe shugaban na Boko Haram a yankin Sambisa yayin wata arangama da ISWAP, wacce rahotanni suka nuna ta jima tana so ta kama shi da ransa.

Rahotanni sun ce Shekau ya kashe kansa ne ta hanyar ta da bam din da ke jikinsa, bayan da aka rutsa shi.

Jaridar Punch wacce ita ma ta ruwaito labarin mutuwar shugaban kungiyar ta Boko Haram, ta dangantaka labarinta da rahoton da wata kafar yada labarai mai suna HumanAngle ta fitar.

Me Hukumomin Tsaro Ke Cewa?

Kawo yanzu, babu wata hukumar tsaro a Najeriya da ta tabbatar da gaskiyar wannan al’amari.

Ganawar Shugaba Buhari da Shugabannin Tsaro 3
Ganawar Shugaba Buhari da Shugabannin Tsaro 3

Amma wasu rahotanni sun ce hukumomin tsaron na kan bincike don tabbatar da sahihancin labarin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da rahotanni ke cewa an kashe Shekau ba.

Karin bayani akan: ISWAP, ​Boko Haram, Abubakar Shekau, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Dakarun Najeriya, sun sha ikirarin cewa sun kashe shi, amma sai a gan shi ya bayyana a bidiyo ko ya saki wani faifan muryarsa yana karyata hukumomin tsaron kasar.

Abin Da Masu Bincike Kan Al’amuran Tsaro Ke Cewa

Masu sharhi kan al’amuran tsaro da bincike kan ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda irinsu Barrister Bulama Bukarti sun ce, suna bin diddigin rahotannin da ke nuna cewa an kashe Shekau.

“Ina bibiyar rahotannin da ke cewa kungiyar ISWAP ta kashe Shekau. Labarin yana nuna kamar da gaske ne, amma dai ban tabbatar da shi daga bangarena ba.” Bukarti ya rubuta a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Ya kara da cewa, “idan har an kashe wannan dadadden shugaban ‘yan ta’adda, hakan zai samar da gagarumin sauyi.”

A shekarar 2016, rundunar sojin ta Najeriya ta yi ikirarin jikkata Shekau da wani mummunan rauni a wasu hare-hare da ta kai a dajin Sambisa.

Wani abu da ya saba ikirarin kisan Shekau a wannan karo shi ne, ba sojoji ba ne suka ce sun kashe shi.

Kungiyar na gudanar da ayyukanta ne a yankin Tafkin Chadi kamar yadda Boko Haram take yi - duk da cewa sun bangare.

A shekarar 2016, ISIL ta ayyana Abu Musab-Albarnawi a matsayin shugaban kungiyar baya da Boko Haram ta yi mubaya’a da kungiyar ta ISIL, lamarin da Shekau bai yi na’ama da shi ba, ya kuma kai ga bangarewar kungiyar zuwa gida biyu.

Gwamnatin Amurka ta taba saka tukwicin dala miliyan 7 (Naira biliyan 2.5) ga duk wanda ya ba da bayanan da za su kai ga kama Shekau.

XS
SM
MD
LG