Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar 'Yan bindiga: An Kaddamar Da Rundunar 'Yan sintiri Ta Musamman A Jihar Neja


A kokarin yaki da 'yan bindiga da suka addabi jihar Nejan Najeriya, gwamnatin jihar ta kaddamar da wata rundunar sintiri da ta baiwa horo na musamman ta yadda za ta yi yaki da wadannan 'yan bindiga.

Gwamnatin jihar Nejan ta ce ta samar da wadannan 'yan sintiri ne da za su gudanar da aiki da jami'an tsaro, abin da ta ce zai taimaka a kokarinsu na kawar da 'yan ta'adda da suka addabi jihar Nejan in ji Kwamishinan kananan Hukumomi da Masarautu na jihar Barista Abdulmalik Sarkin Daji da ya Wakilci Gwamnan Jihar a wajan kaddamar da wadannan 'yan sintiri.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Nejan Alh. Adamu Usman, ya ce sun zabo 'yan sintirin ne daga kungiyoyin dake taimakawa jami'an tsaro a jihar kuma sun ba su horo kamar yadda ya kamata.

Nasiru Muhammad Manta shi ne kwamandan kungiyar 'yan banga a jihar Nejan ya kuma ce za su yi aiki domin tabbatar da ganin bayan 'yan ta'adda da suka addabi jihar Nejan.

Gwamna Abubakar Sani Bello, yayin da yake bayani kan muhimmancin samar da 'yan sintiri a wani taro na daban (Twitter/Gwamnatin Neja)
Gwamna Abubakar Sani Bello, yayin da yake bayani kan muhimmancin samar da 'yan sintiri a wani taro na daban (Twitter/Gwamnatin Neja)

A baya, gwamna Abubakar Sani Bello, ya sha alwashin ganin an samar da irin wannan kungiya ta 'yan sintiri, a wani kokari da ya ce gwamnatinsa na yi don ganin karafaf matakan tsaro a jihar.

Ya kuma kara da cewa, 'yan sintirin, za su yi aiki ne kafada da kafada da jami'an tsaro.

A yanzu al'ummar jihar Nejan na cike fatar ganin samar da wadannan 'yan sintiri ya kawo canji ta fuskar tsaron.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

XS
SM
MD
LG