Tun da farko, Majalisar Dattawan Brazil ta kada kuri'ar tsige Rousseff da 61 akasin 20, saboda saba ma dokar kasafin kudin gwamnatin tarayya.
Wannan sakamakon ya zo ne bayan da Rousseff, wadda ita ce mace ta farko da ta Shugabanci kasar, ta fuskanci tambayoyi na tsawon sama da sa'o'i 14 ranar Litini. An yi muhawarar karshe ta tsige ta ne ranar Talata. Kafin tsigewar ta yi tasiri, sai akalla 54 daga cikin Sanatoci 81 sun kada kuri'ar tsigewar.
Da ya ke jawabi a wani taron jami'an gwamnatinsa da aka yada ta gidan talabijin, Temer ya ce batun farfado da tattalin arzikin Brazil, da janyo masu saka jari daga kasashen waje, da rage rashin ayyukan yi, da gyara fannin fensho su ne zai maida hankali a kai.
An zargi Rousseff da amfani da kudaden da ke bankunan gwamnati wajen boye gibin da aka samu a kasafin kudi, don ta yi farin jini yayin da ake dosar zaben Shugaban kasa na 2014, zargin da ta karyata.