McCain dan shekaru 80 da haifuwa yana kokarin samun wa'adi na shida a majalisar dattijan inda yake wakiltar jihar Arizona dake kudu maso yammacin Amurka. Ya doke wata daga banagaren 'yan gwagwarmayar Tea party, yanzu zai kara da 'yar majalisar wakilai ta jam'iyyar Democrat Ann Kilpatrick a zaben kasa da za'a yi cikin watan Nuwamba.
Rubio wanda kokarinsa na zama dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Republican bai sami nasara ba, shima zai kara da dan majalisar wakilai na jam'iyyar Democrat,bayan ya doke wani hamshakin attajiri Carlos Beruff wanda yayi kudi ta wajen gina gidaje, a zaben fidda dan takara da aka yi jiya Talata a jihar Flroida. Rubio zai kara da dan majalisa wakilan Amurka Patrick Murphy.
Haka nan a jahar ta Florida Debbie Waserman Schultz ta lashe zaben zama 'yar takara, wata daya bayan da ta yi murabus daga zama shugabar jam'iyyar Democrat.
Za'a yi zaben wakilan majalisar ne lokaci daya da zaben shugaban kasa ranar 8 ga watan Nuwamba. Sulusi na majalisar dattijai ne zasu sake yin takara, yayinda illahirin 'yan majalisar wakilai su 435 za'a yi zabe na wadanan kujerun duka. Ahalin yanzu dai jam'iyyar Republican ce take da rinjaye a duka majalisun biyu.