Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci a Najeriya Ibrahim Magu ne ya bayyana haka a zantawa ta musamman da Muryar Amurka.
Magu yace hukumar EFCC tun farko ta mika bukata ga rundunar ‘yan sandan ta kasa da kasa ‘INTERPOL” kan neman kama Adoke wanda ke gudun hukunci ko gurfana gaban kotu a Najeriya.
Yanzu dai EFCC za ta tura bayanan tuhuma ga “Interpol” din a Daular Larabawa don isarwa ga Adoke kan tuhumar zarmiya da kudin Najeriya.
Magu ya ce za a bukaci dawo da Adoke Najeriya don hukunta shi.
Hakanan mukaddashin shugaban na EFCC yace yanzu ba wata mafaka da barayin biro za su samu a fadin duniya don yarjejeniya ta dawo da wanda a ke tuhuma don fuskantar shari’a.
EFCC tace zata mika bukatu ga taron shugabannin kasashe don karfafa yarjejeniyar dawo da duk wanda ya arce bayan aikata laifi don fuskantar tanadin doka.
Facebook Forum