Rundunar ‘yan sandan ta kasa-da-kasa wadda mazauninta ke Faransa, ta riga ta kama mutane 26 a kasashe da yawa a bisa zargin suna da hannu a batun fasa kwaurin baki 'yan cin rani.
Daraktan kungiyar ‘yansandan na kasa-da-kasa Michael O’Connell, ya ce kungiyoyin masu laifin fasa kwaurin ba sa kulawa da lafiyar mutane wadanda suke wa kallon tamkar wani abun saidawa ne a garesu, kamar yadda abin ya bayyana a kasashe da dama na duniya.
‘Yan sandan sun fidda hotunan mutanen su 11 da ake zargi a shafin su na yanar gizo yau Alhamis, inda kuma suke kira akan duk mai wani bayani game da su ya fito ya fada masu; koda ya ke, sun jaddada cewa, kama masu fasa kwaurin baki mawuyacin abu ne, saboda yawancin lokuta wadanda aka yi fasa kwaurin ba sa so su ba da bayani.
Wadanda ake zargi da yin simogal din baki na samun tarin kudade masu yawa akan kowanne mutum da suka ce za su kai kasar Turai, akwai wata kungiyar masu fasa kwauri ta ‘yan Albania da ke cajin har dala 16,000 akan duk wanda za su kai Ingila daga Faransa cikin kwalakwale.